Jam'iyyar NNPP a Katsina ta ce ta shirya tsaf domin lashe zaɓen ƙananan hukumomi
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Monday, 02 Sep, 2024
Jam'iyyar NNPP a Katsina ta ce ta shirya tsaf domin lashe zaɓen ƙananan hukumomi
Jam’iyyar NNPP, ta bayyana aniyar ta na lashe kujerun shugabanni ƙananan hukumomi da kansiloli a zaɓen ƙananan hukumomin za a gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairun 2025 a jihar Katsina.
Shugaban jam’iyyar a jihar, Armaya’u Abdulkadir ne ya bayyana hakan a Katsina ranar Asabar, yayin da yake ƙaddamar da sabon zama da ya shafi jam'iyyar da kuma canja logon jam'iyyar.
A cewarsa, jam’iyyar ta shirya tsaf domin shiga zaɓen shugabancin ƙananan hukumomi da kansiloli don ganin sun cinye duka zaɓukan a jihar.
Kamar yadda Katsina Post ta samu daga NAN cewa, a ranar 14 ga watan Fabrairu ne hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar ta sanya ranar 15 ga watan Fabrairun 2025 a matsayin ranar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar.
Shugaban ya ce, jam'iyya mai mulki fom ɗin da ta sayar ya yi ma 'yan jam'iyyar tsada a takara a dukkan ƙananan hukumomi 34, ya ce ta dalilin haka ne a kan fushin da wasu suka yi ya sa su goya ma su baya.
Ya jaddada cewa, da yardar Allah suna sa ran nasara, domin babu wata jam'iyya da zata iya kada su zaɓe.