Hukumar SUBEB Ta Ja Kunnen Shugabannin Makarantun Kan Siyar Da Lalatattun Kujerun Zama Babu Ka'ida
- Posted By: Sadiq Bindawa --
- Monday, 21 Oct, 2024
Hukumar SUBEB ta ja kunnen shugabannin makarantu kan siyar da lalatattun kujeru babu ka'ida
Hukumar Ilimin bai-ɗaya ta jihar Katsina, SUBEB ta ja kunnen shugabannin makarantun firamare kan siyarda dukkanin kujerun da suka lalace ba bisa ka'ida ba.
Shugaban hukumar, Dr. Kabir Magaji Gafia ne yayi jan kunnen da yake fira da gidan radiyon Alfijir.
Dr. Kabir Magaji ya bayyana cewa matakin da shugabannin ke ɗauka ya saɓa ma doka kuma yana matukar damun sa.
Yace hukumar na samun korafe-korafe na sace kujerun zama da sauran ababen ƙarfe don siyarwa.
Yace sau da yawa Gwamnati za ta samar da isassun kujeru sai kuma a siyar babu ka'ida ko a sace bayan watanni.
Sai dai yace hukumar ta fara ɗaukar matakin magance matsalar na tabbatar da bin diddiƙin dukkanin kujerun dake kowace makaranta.
Yace shugabannin makarantun su tabbatar sun killace dukkanin kujerun zaman da suka lalace, kuma za'a saida a hukumance domin gyara wasu.
Daga nan Dr. Kabir Magaji ya bayyana cewa Gwamnati na bakin kokarin ta na samar da kujeru zaman ɗalibai a makarantun amman matsalar ta haifar da koma baya.