Gwamnatin tarayya ta sauke Abbas Masanawa daga mukamin sa
Gwamnatin tarayya ta sauke Abbas Masanawa daga mukamin sa
- Posted By: Mustapha Saddiq --
- Monday, 02 Sep, 2024
Gwamnatin tarayya ta sauke Abbas Masanawa daga mukamin sa
Babban bankin Najeriya, ya sanar da sauke dukkan shugabannin gudanarwar bankin bayar da lamuni ga manoma a Najeriya watau Nigeria Incentive-Based Risk Sharing System for Agriculture Lending (NIRSAL) daga mukamin su.
Kamar yadda Katsina Post ta samu, wadanda wannan hukuncin ya shafa sun haɗa da shugaban bankin, Alhaji Abbas Umar Masanawa da dukkan daraktocin bankin.
Abbas Masanawa dai ɗan jihar Katsina ne kuma ya nemi tikitin takarar kujerar Gwamnan jihar Katsina a karkashin jam'iyyar APC a zaɓen da ya gabata.
Kawo yanzu dai, babban bankin na Najeriya bai bayyana dalilin tsige su ba.
Ko watannin baya dai Babban bankin ya yi ma wasu manyan ma'aikatan sa ritayar dole a wani mataki da yace yana dauka domin tsaftace bankin.
Source: The Cable: https://www.thecable.ng/cbn-sacks-nirsal-md-directors/amp/