Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Sabbin Jiragen Yaƙi 2 A Katsina
An Ƙaddamar Da Sabbin Jiragen Yaƙi 2 A Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Saturday, 23 Nov, 2024
Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Sabbin Jiragen Yaƙi 2 A Katsina
An ƙaddamar da sabbin jiragen yaƙi 2 daga gwamnatin tarayya ta hannun ministan tsaron Najeriya a Katsina.
Tunda farko, Ministan Tsaro a Najeriya, Alhaji Badaru Abubakar, ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba za a shawo kan matsalolin tsaro da ƙasar nan ke fuskanta.
Kamar yadda Katsina Post ta samu daga The Triumph, Ministan tsaron tare da babban hafsan hafsoshin sojin sama Air Marshal Hassan Bala Abubakar, sun tabbatar da haka a lokacin ƙaddamar da wasu ƙarin jirage masu saukar ungulu a jihar.
A cewar ministan, jirage masu saukar ungulu guda biyu suna da matuƙar muhimmanci da fa'ida fiye da sauran jiragen yaƙi, tare da tabbatar da cewa babu wani ɗan ta'adda da zai tsira zuwa nan gaba kaɗan a jihar. Ya jaddada cewa an tura jirage masu saukar ungulu na musamman domin yakar ‘yanbindiga da sauran miyagun laifuka da ke barazana ga zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaban yankin Arewa maso Yamma wanda daga ciki har da jihar Katsina.
Ministan ya kuma yaba da jajircewa, sadaukarwa, da sojojin suka yi a ci gaba da gudanar da ayyukan tabbatar da makomar Najeriya, inda ya ce tuni ƙoƙarin su ya haifar da ɗa mai ido.
Ya ƙara da cewa an samu ci gaba sosai, manoma sun koma gonakinsu, yara na komawa makaranta, sana’o’i suna ci gaba da bunƙasa.