Gwamnatin Jihar Katsina ta hana zanga-zanga, ta sanya dokar ta ɓaci

Gwamnatin Jihar Katsina ta hana zanga-zanga, ta sanya dokar ta ɓaci

FB_IMG_1721457855592_1

Gwamnatin Jihar Katsina ta hana zanga-zanga, ta sanya dokar ta ɓaci


Muƙaddashin Gwamnan Jihar Katsina Malam Faruk Lawal Jobe ya sanya dokar ta-ɓaci ta tsawon awanni 24 a ƙaramar hukumar Dutsanma, a yayinda aka sanya dokar ta ɓaci daga 7 na dare zuwa 7 na safe a dukkanin sauran ƙananan hukumomi 33 na jihar.

Haka zalika a dokar da bayar, Malam Faruk Lawal Jobe ya kuma hana duk wani taro da duk wani nau'i na zanga-zanga a faɗin jihar .

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Ƴan Jarida na Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina Barista Abdullahi Garba Faskari, wanda Abdullahi Aliyu Ƴar'adua ya sanya wa hannu, inda ya bayyana cewa, an dauki matakin ne a taron gaggawa na tsaro da aka gudanar akan rahoton da aka samu na karya doka da oda a wasu sassan jihar a dalilin zanga-zanga.

Sanarwar ta ƙara dacewa, mukaddashin Gwamnan ya karbi wasu kungiyoyin Fararen hula da suka gabatar da zanga-zangar lumana a gidan Gwamnati, inda ya sha alwashin kai korafin su ga Inda ya dace.

Haka zalika, Gwamnati ya samu rahoton yadda wasu ɓata gari suka yi amfani da zanga-zangar tare karyawa mutane shaguna da sace-sace gami da lalata kayayyakin gwamnati da na al'umma.

A dalilin haka, Gwamnati taga dole ta ɗauki matakin domin kiyaye rayukan da dukiyoyin al'umma.

An kuma gargadi mutane da su zama masu bin doka da oda a yayinda aka umarci jami'an tsaro da su kama duk wani mutum ko wata ƙungiya da aka samu ya karya dokar.


Mukaddashin Gwamnan ya kuma yi kira ga al'ummar jihar nan da su cigaba da harkokin a lokacin da aka basu na walwala.


Comment As:

Comment (0)