Gwamnatin Dikko Radda Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 30 Kan Tsaro
Dikko Raɗɗa ya kashe sama da Biliyan 30 kan inganta tsaro
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Monday, 02 Sep, 2024
Gwamnatin Dikko Radda Ta Kashe Sama Da Naira Biliyan 30 Kan Tsaro
A gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa, an kashe sama da Biliyan 30 cikin watanni 15 don magance matsalolin tsaro a jihar.
Gwamnatin jihar ta sanar da haka a ranar Lahadin da ta gabata kan kashe sama da Naira Biliyan 30 a cikin watanni 15 da suka gabata don yaƙi da matsalar rashin tsaro da ta addabi ƙananan hukumomin da suke fama da Iftila'in tsaro.
Kwamishinan tsaron cikin Gida Dr. Nasiru Mu'azu Danmusa, shi ne ya bayyana haka a yayin taron masu ruwa da tsaki a shiyyar Funtua, wanda a ka gudanar cikin ƙaramar hukumar Funtua.
Taron dai shi ne na farko cikin tarurruka uku da nufin tattara ra’ayoyin jama'a don daidaita ƙudirin kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025, wanda za a gabatar da shi ga majalisar dokokin jihar nan da watanni masu zuwa.
Da yake magana gameda tashe tashen hankulla tun daga ranar 29 ga watan Mayu 2023 zuwa yau, kwamishinan ya bayyana cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta ga matsalar tsaron gwamnatin jihar ta samu nasarori kaɗan daga ciki.
A cewar sa, sama da Matasa 1,500 ne aka ɗauka aiki a ƙarƙashin jami'an tsaron cikin gida KSCWC na jihar don taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙi da ‘yanbindiga a yankunan, tare da ɗaukar ƙarin wasu jami'an aiki da za su ƙara yawa ga ayyukan, wanda aka ware alawus-alawus don kula da su a kowane wata.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, gwamnati na ware Naira Miliyan 3 duk wata ga shugabannin ƙananan hukumomin domin biyan kayan aikin da ake buƙata domin yaƙi da rashin tsaro.
Ya kuma ba da tabbacin cewa, gwamnatin a shirye take ta saurari matsalolin al'umma da ke fuskantar ƙalubalen tsaro tare da bayar da tallafin da ya dace.