Gwamna Dikko Radda zai kai ya'yan talakawa 68 ƙasar China domin yin karatu

Gwamna Dikko Radda zai kai ya'yan talakawa 68 ƙasar China domin yin karatu

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

FB_IMG_1724015815707_1

Gwamna Dikko Radda zai kai ya'yan talakawa 68 ƙasar China domin yin karatu 

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Mallam Dikko Umar Radda zai sake kai wasu ƴan asalin jihar mutum 68 zuwa ƙasar Sin (China) domin su yi karatu.

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Farouk Lawal Jobe ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi a wurin taron jin ra'ayin jama'a kan kasafin kudin shekarar 2025 dake tafe da aka gudanar a garin Daura.

A cewar sa, ranar 13 ga watan Satumba ne dai ɗaliban za su tafi kuma tuni gwamnatin jihar ta biya masu kuɗin makarantar su da dukkan sauran bukatun su har zuwa lokacin da za su dawo.

Haka zalika a ce ɗaliban za su fito ne daga cikin ya ƴan talakawan jihar dalibi biyu daga kowace karamar hukuma.