Gwamna Dikko Radda ya samu sama da Naira biliyan 60 daga gwamnatin tarayya a shekarar 2024

Gwamna Dikko Radda ya samu sama da Naira biliyan 60 daga gwamnatin tarayya cikin wata shida

Gwamna Dikko Radda ya samu sama da Naira biliyan 60 daga gwamnatin tarayya cikin wata shida

Akalla sama da Naira miliyan dubu shidda ne gwamnatin jihar Katsina, karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ta karba daga gwamnatin tarayyar Najeriya a cikin wata shidda na farkon wannan shekarar ta 2024, kamar yadda wasu alkalumma suna bayyana.

A cikin wani jaddawali da kungiyar nan wadda ba ta gwamnati ba, BudgIT ta wallafa ta bayyana cewa jihar ta Katsina ta samu akalla Naira biliyan sittin da miliyan 100 daga watan Janairu zuwa na Yuni na wannan shekarar.

Wannan dai na a matsayin kimanin Naira biliyan 10 kenan duk wata a ma'aunin kiyasi.

Duk wata dai akwai wasu kudade da gwamnatin tarayya ke rabawa ga gwamnatocin jahohi da na kananan hukumomin kasar.

KARANTA KUMA: GWAMNA DIKKO RADDA YA NEMI TINUBU YA BA SHI AIKIN WUTAR LANTARKIN LAMBAR RIMI YA IDA

Duk dai a jadawalin alkalumman da BudgIT din ta wallafa jihar Delta ce ta fi kowa samun kaso mai tsoka daga kudaden inda ta samu akalla Naira biliyan 260 yayin da jihar Ogun kuma ta samu mafi karanci na kudin Naira biliyan 40.

Haka zalika alkalumman sun nuna cewa a duka arewacin Najeriya, jahohin Kano da Borno ne kawai suka fi jihar Katsina samun kudaden daga gwamnatin tarayya a cikin watanni shida din inda jihar Kano ta samu sama Naira biliyan 157 ita kuma jihar Borno ta samu sama da Naira biliyan 63. 

Source: BudgIT

Comment As:

Comment (0)