Gwamna Dikko Radda Zai Jagoranci Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar Edo Na APC
Gwamna Dikko Radda Zai Jagoranci Yakin Neman Zaben Gwamnan Jihar Edo Na APC
- Posted By: Mustapha Saddiq --
- Friday, 02 Aug, 2024
Gwamna Dikko Radda Zai Jagoranci Babban Kwamitin Yakin Neman Zaben Dan Takarar Gwamnan Jihar Edo A Karkashin Jam'iyyar APC
Uwar jam'iyyar APC ta kasa, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta amince da naɗa gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda a matsayin wanda zai jagoranci babban kwamitin yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Edo a karkashin jam'iyyar APC mai dauke da sunayen jajirtattun ya'yan jam'iyyar APC dari da tis'in da bakwai da aka zabo daga sassa daban-daban a fadin Najeriya.
KU KARANTA KUMA: WANI DAN BINDIGA YA JI WUTA YA TUBA A KATSINA, YA KAWO KAN SA WURIN GWAMNATI
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwar jerin sunayen mutanen da uwar jam'iyyar APC ta fitar, wadda sakataren tsare-tsaren jam'iyyar APC na kasa Alhaji Sulaiman Muhammad Argungu ya sanya wa hannu aka rabawa manema Labarai a birnin Tarayya, Abuja yau Laraba.
Uwar jam'iyyar APC ta kasa ta zabo zakukuran mutane daga kowane sashen Najeriya kuma masu gogewa a fannoni daban-daban, wanda gwamnan jihar Cross River Mista Bassey Eddy Otu ta naɗa a matsayin shugaban babban kwamitin gudanarwar yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Edo da za'a gudanar a watan Satumba na wannan shekarar.
A cikin yan kwamitin na ya'yan jam'iyyar APC na mutane dari da Tis'in da bakwai (197) akwai tsohan gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da babban mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Masari da Kwamishinan lafiya na jihar Katsina, Honarabul Musa Adamu Funtua da kuma tsohan shugaban Asusun Bunkasa Harkokin Man Fetur (PTDF) Injiniya Dakta Muttaka Rabe Darma duk daga jihar Katsina.