Farashin Barkono Ya Faɗi Ƙasa Warwas A Kasuwannin Katsina
Jerin yadda farashin Abinci yake a jihar Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Wednesday, 25 Sep, 2024
Farashin Barkono Ya Faɗi Ƙasa Warwas A Kasuwannin Katsina
Farashin Barkono ya yi ƙasa wanwar, inda ya koma 120,000 a wasu kasuwannin jihar Katsina.
Kasuwar garin Danmusa, ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun Masara - 60,000
2- Buhun Dawa Fara - 70,000
3- Buhun Gero - 67,000
4- Buhun Wake manya - 130,000
5- Buhun Waken suya - 160,000
6- Buhun Alabo - 75,000
7- Buhu Ridi - 140,000
Kasauwar garin Kankara ga yadda farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara - 75,000 sabuwa 45,000 zuwa 46,000
2- Buhun Dawa - 80,000
3- Buhun Gero - 80,000
4- Buhun Shinkafa samfarera - 41000
5- Buhun Gyada - 150,000
6- Buhun wake tsoho - 195,000 zuwa 200,000 sabo manya - 65,000 zuwa 67,000 kanana - 145,000
7- Buhun Waken suya -
8- Buhun Alkama - 115,000
9- Buhun Alabo - 57,000
10- Buhun Barkono Dan zagade - 60,000 busasshe - 140,000 Mai Kore - 30,000
11- Buhun Albasa - 50,000
12- Buhun Goro fari marsa - 38,000 Tiyar - 9,000 menu - 27,000 tiya - 8,000
13- Buhun Tattasai - 20,000
Kasuwar garin Mashi, ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun Masara - 85,000 sabuwa - 56,000
2- Buhun Dawa - 90,000
3- Buhun Gero - 74,000
4- Buhun Waken suya sabo - 112,000
5- Buhun Wake - 120,000
6- Buhun Alkama - 100,005
7- Buhun Albasa - 92,000
8- Buhun Aya kanana - 84,000
9- Buhun Alabo - 72,000
10- Buhun Tattasai kauda - 140,000
11- Buhun Barkono - 150,000
12- Buhun sobo - 20,000
Kasuwar garin Ajiwaa karamar hukumar Batagarawa,ga yadda farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara - 80,000 sabuwa - 63,000
2- Buhun Dawa - 80,000
3- Buhun Gero - 88,000
4- Buhun Barkono - 120,000
5- Buhun Tarugu - 26,000
6- Buhun Alabo - 70,000
7- Buhun Dussa Fara - 28,500 ja - 24,500 kowa - 18,500
8- Buhun Garin kwaki - 50,000
9- Buhun Dankali - 21,000
20- Buhu hakin gyada - 3,000_4,000
Kasuwar garin Bakori,ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun masara - 78,000 sabuwa - 60,000
2- Buhun Dawa - 80,000
3- Buhun Gyada - 160,000 Mai bawo - 50,000
4- Buhun Shinkafa tsaba - 140,000 shanshera - 50,000
5- Buhun Wake kanana - 145,000 sabo - 67,000
6- Buhun waken suya sabo - 115,000
7- Buhun Alabo - 67,000
8- Buhun Barkono - 200,000 sabo ja - 180,000
9- Buhun Albasa - 60,000
10- Buhu Alkama - 112,000
11- Buhun Tarugu - 40,000
12- Buhun Albasa - 55,000 zuwa 60,000
Kasuwar garin Funtua,ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun masara - 83,000 sabuwa - 52,000 zuwa 56,000 ya danganta da yanayin bushewarta
2- Buhun Dawa - 90,000 _ 92,000
3- Buhun Gero - 70,000 zuwa 90,500
4- Buhun waken suya - 105,000 zuwa 106,000
5- Buhun shinkafa - 52,000_55,000 tsaba - 140,000 zuwa 160,000
Daga Aysha Abubakar Danmusa.