Farashin Abinci Ya Fara Yin Sauƙi A Kasuwannin Jihar Katsina
An fara samun sauƙin farashin Abinci a Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Monday, 02 Sep, 2024
Farashin Abinci Ya Fara Yin Sauƙi A Kasuwannin Jihar Katsina
Farashin kayan abinci ya Fara sauka, ganin cewa kaka ta Fara bullo Kai inda sabuwar Masara take 60,000 zuwa 70,000 tsohuwa Kuma 92,000 a wasu kasuwannin jihar Katsina
Kasuwar garin Rimaye, a karamar hukumar Kankiya, ga yadda farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara - 88,000 sabuwa - 70,000
2- Buhun Dawa fara - 80,000 ja - 80,000
3- Buhun Gero tsoho - 80,000 sabo - 60,000 Dauro - 90,000
4- Buhun Shinkafa - 165,000 shenshera - 55,000
5- Buhun Gyada - 160,000
6- Buhun Wake - 160,000 sabo - 120,000
7- Buhun Waken suya - 110,000
8- Buhun Tattasai Kauda - 264,500
9- Buhun Kalwa - 64,000
10- Buhun Barkono - 200,000
10- Buhun Alabo - 90,000
11- Buhun Kalwa - 64,000
12- Buhun Dabino - 140,000
Kasuwar garin 'Yantumaki a karamar hukumar Danmusa, ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Buhun Masara sabuwa - 65,000
2- Buhun Dawa - 80,000
3- Buhun Gero sabo - 65,000
4- Buhun Dauro - 88,000
5- Buhun Gyada - 126,000
6- Buhun Shinkafa tsaba - 170,000 shanshera - 60,000
7- Buhun Wake tsoho - 170,000 sabo - 120,000
8- Buhun waken suya - 120,000
9- Buhun Aya - 58,000
10- Buhun Ridi - 140,000
11- Buhun Kalwa - 60,000
12- Buhun Alkama - 100,000
13- Buhun Albasa - 35,000
14- Buhun Rogo - 60,000
15- Buhun Tattasai - 53,000 solo - 28,000
16- Buhun Alabo - 60,000
Kasuwar garin Dandume, ga yadda Farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara fara - 85,000 ja - 90,000
2- Buhun Dawa - 88,000
3- Buhun Gero - 75,000 Dauro - 78,000
4- Buhun Shinkafa - 150,000 samfarera - 65,000 ta tuwo - 175,000
5- Buhun Gyadar kulli - 135,000_185,000 ja - 170,000 Mai bawo - 60,000
6- Buhun Wake - 180,000 ja - 195,000
7- Buhun waken suya - 105,000
8- Buhun Rogo - 83,000
9- Buhun Alkama - 92,000
10- Buhun Tumatur Kauda - 150,000
11- Buhun Tattasai Kauda - 200,000
12- Buhun Aya manya - 115,000 kanana - 90,000
13- Buhun Albasa - 40,000
14- Buhun Kubewa - 50,000
15- Buhun Barkono - 150,000
Kasuwar garin Safana ,ga yadda farashin sa yake kamar haka;
1- Tiyar masara - 2,200 sabuwa - 1,800 ja - 1,700
2- Tiyar Dawa Fara - 2,000 ja - 2,000
3- Tiyar Gero - 2,000 sabo - 1,500 zuwa 1,600
4- Tiyar wake sabo - 3,500
5- Tiyar waken suya - 3,000
6- Tiyar Gyadar - 3,100 sabuwa Mai bawo - 1,500
7- Tiyar Ridi - 2,000
8- Buhun Rogo - 1,700
Kasauwar garin Charanchi, ga yadda Farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara tsohuwa - 92,000 sabuwa 60,000
2- Buhun Dawa - 88,000
3- Buhun Gero - 68,000 zuwa 80,000
4- Buhun Shinkafa - 170,000
5- Buhun Gyada - 155,000
6- Buhun wake - 150,000_160,000 sabo - 140,000
7- Buhun waken suya - 110,000_120,000
8- Buhun Alabo - 88,000
9- Buhun Garin kwaki - 50,000
Kasauwar garin Mai'adua, ga yadda Farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara tsohuwa - 90,000
2- Buhun Dawa - 88,000
3- Buhun Gero - 88,000
4- Buhun Shinkafa - 157,000
6- Buhun Wake - 185,000 sabo - 120,000
7- Buhun waken suya - 120,000
8- Buhun Alabo - 100,000
9- Buhun Alkama - 120,000
10- Buhun tattasai - 35,000
11- Buhun Tarugu - 30,000
12- Buhun Albasa sabuwa - 30,000
Kasuwar garin Dutsi,ga yadda Farashin sa yake Kamar haka;
1- Buhun Masara - 92,000 ja - 92,000 sabuwa - 70,000
2- Buhun Dawa 'yar kudu - 83,000 Mori - 83,000 ta gida - 81,000 farfara - 81,000
3- Buhun Gero tsoho - 86,000 sabo - 65,000 Maiwa - 86,000
4- Buhun Shinkafa -
5- Buhun Wake - 150,000 ja - 135,000
6- Buhun Barkono tsoho - sabo - 80,000
Daga Aysha Abubakar Danmusa.