Dikko Radda Da UNICEF Za Su Yaƙi Yunwa Da Naira Miliyan 400 A Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Friday, 06 Sep, 2024
Dikko Radda Da UNICEF Za Su Yaƙi Yunwa Da Naira Miliyan 400 A Katsina
An aƙalla katan 7,000 na abincin ƙananan Yara da gwamnatin Malam Dikko Umaru Raɗɗa za ta yaƙi matsalar ingantaccen Abinci mai gina jiki ga ƙananan Yara a jihar.
Gwamnatin jihar Katsina haɗin guiwa da Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) sun yi wani yunƙuri na kashe Naira Miliyan 400 don magance matsalar rashin ingantaccen Abinci Yara mai gina jiki da ake fama da su a jihar.
Kamar yadda Katsina Post ta samu daga Thisday, a lokacin da wakilin UNICEF a ƙasar ya ziyarci Katsina, Cristian Mundauate, wanda ya bayyana haka a ranar Laraba a lokacin da yake miƙa kayan tallafin ga gwamnatin jihar Katsina, ya ce za su bayar da tallafin ceto rayukan Yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar aƙalla su 8,000 da ke fama da tamowa a jihar.
A cewar sa tallafin kayan abincin dai haɗin guiwa ne da gwamnatin jihar Katsina da kuma UNICEF, inda suka sanyo tallafin ta hanyar asusun ciyar da Yara abinci mai gina jiki, ya ce duk hakan na a cikin ƙudirin hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya na magance matsalar rashin ingantaccen Abinci mai gina jiki da sauran matsalolin da ke addabar ƙananan yara a jihar.
Da ya ke karbar katan-katan din abincin, gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya ce jihar Katsina na da yawan yaran da ke fama da tamowa sosai, ta dalilin haka ne gwamnatin jihar da asusun kula da ƙananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya zai inganta lafiyar yaran da kuma kawar da annobar a jihar.
A cewar sa, gwamnatin jihar da UNICEF sun kashe kimanin Naira Miliyan 400 na kuɗaɗen samar da abubuwan gina jiki ga Yara daga shekaru biyar abinda ya yi ƙasa, inda ya ce magance matsalar rashin Abinci mai gina jiki ga ƙanana Yara a jihar, yana ɗaya daga cikin babban burin gwamnatinsa.