Ayyukan ta'addanci sun ragu sosai a Katsina - Gwamna Radda
Ta'addanci ya ragu sosai a Katsina - Gwamna Radda
- Posted By: Mustapha Saddiq --
- Saturday, 07 Sep, 2024
Ta'addanci ya ragu sosai a Katsina - Gwamna Radda
Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa jihar na ganin raguwar ta'addanci a jihar.
Ya alakanta raguwar kai hare-hare a jihar a lokacin damina da haɗin gwiwar jami'an tsaro a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da ya amshi baƙuncin Hafsan Sojojin Najeriya Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja a ofishin sa dake a ranar Juma'a, inda ya bayyana farin cikin cewa kashi 90 na ƙasar noma anyi Noman ta a wannan shekarar.
Da yake yabawa Sojoji kan samun tsaro a jihar, Radda ya bukaci Rundunar Soji da sauran jami'an tsaro da su ƙara ɓullo da shirye-shirye don tabbatar da cewa Manoma za su iya girbar abinda suka noma tare da kaishi gida.
Gwamnan ya bayyana Ƙorafe-Ƙorafen da jama'a ke yi na ƙin kai masu dauki a lokacin da aka kai masu hare-hare, an magance shi ta hanyar fitar da lambobi domin kiran gaggawa.
Tun da farko, Babban Hafsan Sojojin Kasar yace ya ziyarci jihar domin duba yadda ake gudanar da aikace-aikacen tsaro tare da duba barikoki gami da ta'aziyya ga rasuwar iyalan Yar'adua kan rasuwar Hajiya Dada.
Ya baiwa Gwamnan cewa jami'an soji zasu cigaba da bada goyon baya da haɗin gwiwa da al'umma domin yaƙi da ta'addanci yana mai bayyana haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki.