Ana gudanar da gangamin dakile yaduwar cutar tarin fuka a Katsina

Ana gudanar da gangamin dakile yaduwar cutar tarin fuka a Katsina

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

TBL tarin fuka

Ana gudanar da gangamin dakile yaduwar cutar tarin fuka a Katsina 

Shugaban kula da shirin dakile yaɗuwar cutar tarin Fuka (tarin TB) na jihar Katsina Dr. Mukhtar Aliyu tare da ƴan tawagarsa sun kai ziyarar ganin Ido a garin Dayi na karamar hukumar Malumfashi da kuma Tsiga na karamar hukumar Bakori domin ganin yadda ake gudanar da duba mutanen da suke fama da tari domin a gano masu dauke da tarin fuka a Basu magani kyauta. 

Gamgamin dai an shirya shi ne tare da taimakon Hukumar Lafiya ta jahar Katsina kuma za a gudanar da shi a fadin kananan hukumomi talatin da hudu na jahar. Da yake duba yadda ake aikin, ya yaba da yadda jama'a masu fama da tari Yara da manya, maza da Mata suka fito domin amfana da shirin. 

Dr. Mukhtar Aliyu, ya bayyana cewa sun shirya ziyarar cibiyoyin da ake gudanar da gamgamin ne na awon cutar tarin TB, domin ganewa idonsu yadda jami'an da suke jagorantar shirin suke tafiyar da aikinsu a ƙananan hukumomin.

Dr. Mukhtar Aliyu, ya ƙara da bayyana cewa manufar shirin shine a gano mutanen da suke fama da tarin fuka amma basu san suna da shiba a kuma basu magani kyauta.Wannan shirin zai taimaka so sai wajen dakile yaduwar cutar tarin fuka a jahar Katsina. 

Dr. Mukhtar Aliyu, ya yabama wakilan da suke jagorantar shirin a ƙananan hukumomin shadaya na yankin funtua da a ka gudanar da shirin ya kuma Bada tabbacin cewa za a gudanar da shirin a sauran ka hukomin ishirin da uku da ke yankin Daura da kuma Katsina nan bada jimawa ba. 

Dr Mukhtar Aliyu ya jaddada kudirin bangaren da ke kula da masu fama da Tarin Fuka na jihar Katsina da cigaba da bada ingantacciyar kulawa ga masu fama da ciwon Tarin Fuka a fadin jihar. 

Ya kuma yi kira ga al'umma dasu ke fama da tarin da ya wuce sati biyu da suje asibitocin dake kusa dasu domin a yi masu awon cutar tarin fuka, awon da kuma maganin duk kyauta ne. 

Daga ƙarshe , ya yabama Gwamnatin jihar Katsina a ƙarƙashin Jagorancin Mal. Dikko Umaru Raɗɗa a bisa goyon bayan da take baiwa shirin domin ganin an daƙile cutar a jihar Katsina, dama sauran shirye shirye na inganta sha'anin kiwon lafiya a faɗin jihar.