Ana Neman Hafsoshin Tsaro Da Suyi Murabus Kan Kasa Shawo Kan Matsalar Tsaro
Ana Neman Hafsoshin Tsaro Da Suyi Murabus Kan Kasa Shawo Kan Matsalar Tsaro
- Posted By: Usman Salisu --
- Wednesday, 25 Sep, 2024
Ana Neman Hafsoshin Tsaro Da Suyi Murabus Kan Kasa Shawo Kan Matsalar Tsaro
Wazirin Katsina na 5 Farfesa Sani Lugga ya yi kira ga manyan hafsoshin Najeriya da su yi murabus sakamakon kasa magance matsalar tsaro a ƙasar.
Ya bada shawarar cewa ya kamata a canja su da wadanda suka fisu ƙwarewa da za su iya kare rayukan ƴan Najeriya.
Lugga ya bayyana haka a lokacin da ya halarci taron lakca da Ƙungiyar Ƴan Jarida ta ƙasa reshen jihar Katsina ta shirya domin bikin murnar cikar jihar Katsina shekaru 37 da samuwa.
Ya jaddada cewa sojoji da ƴan sanda abinda ya kamata shine su kare rayuka da dukiyoyin al'umma gami da gano hanyoyin da za'a tabbatar da samar da zaman lafiya.
Lugga ya kuma bayyana cewa idan Gwamnatin Tarayya ba zata iya magance matsalar tsaro ba, to ya kamata a yiwa kundin tsarin mulki gyara tare da baiwa jihohi damar ƙirƙirar ƴan sandan su, yana mai gargadin cewa bai kamata abar al'umma suna ɗaukar mataki don kare kawunan su, wanda wannan na iya haifar da wata matsalar tsaron.
Tunda farko, Mataimakin Gwamnan jihar Katsina Faruk Lawal Jobe ya yabawa ƙungiyar kan shirya taron, sai ya sha alwashin Gwamnatin Jiha na cigaba da aiki da ƴan jarida domin cigaban jihar, yana mai bayyana nasarorin da Gwamnati ta samu wajen ilimi, lafiya da noma da ruwa da ayyukan yi.
Shugaban Ƴan Jarida na Jihar Katsina Tukur Dan Ali ya bayyana cewa taron lakcar zai taimaka wajen magance matsaloli, yana mai yabawa Shugabannin da suka gabata dana yanzu kan ƙoƙarin su wajen cigaban jihar.