An yi kira ga al'umma su riƙa zuwa asibiti domin yin gwajin tarin fuka a Katsina

An yi kira ga al'umma su riƙa zuwa asibiti domin yin gwajin tarin fuka a Katsina

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

Tarin fuka tuberculosis

An yi kira ga al'umma su riƙa zuwa asibiti domin yin gwajin tarin fuka a Katsina 

Shugaban kula da shirin dakile yaɗuwar cutar tarin Fuka (tarin TB) na jihar Katsina Dr. Mukhtar Aliyu ya kai ziyarar ganin Ido a garin kanyar Uban Daba a karamar hukumar Rimi da kuma Kuraye a karamar hukumar Charanchi.

Ziyarar ana yinta ne domin ganin yadda ake gudanar da duba mutanen da suke fama da tari domin a gano masu dauke da tarin fuka a basu magani kyauta. 

Gangamin dai an shirya shi ne tare da taimakon Hukumar Lafiya ta jihar Katsina kuma ana cigaba da gudanar da shi a fadin kananan hukumomi talatin da hudu na jihar. 

Da yake duba yadda ake aikin, Dr Mukhtar ya yaba da yadda jama'a masu fama da tarin yara da manya, maza da mata suka fito domin amfana da shirin. 

Dr. Mukhtar Aliyu, ya ƙara da bayyana cewa manufar shirin shine a gano mutanen da suke fama da tarin fuka alhalin basu san suna da shiba a kuma basu magani kyauta. Wannan shirin zai taimaka sosai wajen dakile yaduwar cutar tarin fuka a jihar Katsina. 

Dr Mukhtar Aliyu ya jaddada kudirin bangaren da ke kula da masu fama da Tarin Fuka na jihar Katsina da cigaba da bada ingantacciyar kulawa ga masu fama da ciwon Tarin Fuka a fadin jihar. Ya kuma yi kira ga al'umma dasu ke fama da tarin da ya wuce sati biyu da suje asibitocin dake kusa dasu domin a yi masu awon cutar tarin fuka, awon da kuma maganin duk kyauta ne. 

Daga ƙarshe , ya yabama Gwamnatin jihar Katsina a ƙarƙashin Jagorancin Mal. Dikko Umaru Raɗɗa a bisa goyon bayan da take baiwa shirin domin ganin an daƙile cutar a jihar Katsina, dama sauran shirye shirye na inganta sha'anin kiwon lafiya a faɗin jihar.