An roƙi Hon. Ibrahim Sani ya sake neman takarar shugabancin Charanchi karo na biyu

Hon. Ibrahim Sani

An roƙi Hon. Ibrahim Sani ya sake neman shugabancin ƙaramar hukumar Charanci 

Gamayyar kungiyoyi a Charanci sun shirya taron gangami domin kira ga Hon. Ibrahim Sani da ya sa ke fitowa neman shugabancin ƙaramar hukumar a karo na biyu a zaɓe me zuwa. 

Hakanan kuma sun sha alwashin haɗa masa gudumuwar kudin sayen form na tsayawa takara kimanin sama da naira miliyan tara.

A yayin gangamin da ya gudana a farfajiyar sakatariya, mutane da dama sun gabatar da jawabai tare da bayyana Hon. Ibrahim Sani Koda, a matsayin mutunen kirki mai gaskiya da amana wanda dukiyar Al'umma bata gabansa.

Acewar sa, Honourable Ibrahim Sani ya samar da abubuwan more rayuwa masu dimbin yawa a karamar hukumar Charanci wadanda Al'ummar karamar hukumar suke alfahari dasu.

Daga cikin nasarorin sun haɗa da inganta ilmi, kiwon lafiya, ruwan sha, tsaro, hanyoyi, samar da jarin sana'a, da bunƙasa tattalin arzikin alummar.

Da yake gabatar da jawabinsa, shugaban kara mar hukumar Hon. Ibrahim Sani Koda ya gode ma gamayyar kungiyoyin da sauran al'ummar ƙaramar hukumar akan wannan karamci da su ka nuna masa.

Sannan yace zai amince da buƙatun su duk da cewa a baya ya yanke shawarar bazai fito ba. 

Yasha alwashin cigaba da samar da ababen more rayuwa da tsaro tare da kawo cigaba a ƙaramar hukumar idan aka sake zaben sa karo na biyu. 


Comment As:

Comment (0)