An rabawa ma su ƙananan sana'o'i murahun sanwa na zamani a Katsina
An rabawa ma su ƙananan sana'o'i murahun sanwa na zamani a Katsina
- Posted By: Usman Salisu --
- Saturday, 23 Nov, 2024
An rabawa ma su ƙananan sana'o'i murahun sanwa na zamani a Katsina
Aƙalla masu 361 suka amfana da murahun sanwa a jihar Katsina a ranar Alhamis, inda aka zaɓo matan da suka amfana daga ƙananan hukumomi 7 a matsayin wani yunkuri na inganta sana'o'i.
Shugaban Gidauniyar Jihar Katsina Ahmed Karfi ya bayyana cewa Gidauniyar Jihar Katsina ce ta rarraba kayayyakin, inda ya bayyana cewa Gidauniyar ta samu nasara a dukkanin kayayyakin da ta taimakawa al'umma.
Ya bayyana cewa Gidauniyar ta bayar da gudummawa ga cigaban ilimin addinin musulunci da na zamani, inda Limamai 37 aka basu wayoyi ɗauke da manhajoji a ciki.
"A ƴan kwanakin nan mun gudanar da wani shiri, inda muka horar da matasa 400 da mata 106 sana'ar saƙa. Mun kuma horar da Malamai 306 na Firamare a faɗin jihar.