An kama wata mata da alburusai cikin motar KTSTA zata kai ma 'yanbindiga a Katsina
- Posted By: Sadiq Bindawa --
- Sunday, 23 Jun, 2024
- Reporter : Sadiq Bindawa
An kama wata mata da alburusai a motar KTSTA zata kai ma 'yanbindiga a Katsina
Jami'an tsaro dake sintiri akan hanyar Abuja sun cafke wata mata a cikin motar KTSTA da harsasai cikin buhu zata kawo ma 'yanbingida a Katsina.
A cikin wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an gano wata mata da tarin alburusai cikin buhu a motar KTSTA daga Abuja tana kokarin kawo ma 'yanbingida a Katsina.
Matar, wadda ta ayyana sunanta, A'isha Abubakar tace an umurce ta da ta kai harsasan ta aje a hanyar garin 'yantumaki dake Karamar hukumar Ɗanmusa.
Sai dai tace bata san cewa aikata hakan laifi bane kuma ba ta tantance waɗanda suka aiko ta ba.
Katsina Post ta ruwaito cewa, ko daren jiya, yan'bindiga sun hallaka mutane da dama da kone dukiyoyi a wani hari da suka kai a garin maidabino a ƙaramar hukumar Ɗanmusa