An kafa dokar hana shan fiye da lita 50 ta fetur a gidajen mai na NNPC a faɗin jihar Katsina
- Posted By: Sadiq Bindawa --
- Tuesday, 01 Oct, 2024
An ƙayyade lita 50 ta man fetur a matsayin iyakar man da gidajen mai na NNPC zata rika ba kowacce mota a jihar Katsina.
Kwamitin kula da Shigowa da rarraba Albarkatun man fetur na jihar Katsina yayi zama da masu Ruwa da tsaki domin kayyade yanda za arika rarraba mai ga Al'ummar Jihar da kewaye
Dayake ma manema labarai jawabi jimkadan bayan kammala zaman Shugaban kwamitin Alh. Muhammad Lawal Aliyu Daura yace anyi Hakane domin tabbatar da kawo dai dai to tsakanin masu shan mai a jihar duba da korafe korafe da ake samu daga Al'umma
Shugaban ya bayyana cewa dokar zatai aiki ne Akan gidajen man NNPC dake jihar Katsina da kewaye madamar ankama wani gidan mai da karya doka ta karkatar da mai ga wasu ƙayyadaddun motaci to hakika doka zata hau kanshi sabili da haka ne aka bayyana lita 50 a matsayin ƙarshen abinda kowacce mota zata sha
Daga karshe yayi kira ga shugabanin gidajen man da su bi doka da oda domin kauce ma fadama fushin kwamitin