An dakatar da sakataren ƙaramar hukumar Jibia
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Friday, 14 Jun, 2024
An dakatar da sakataren ƙaramar hukumar Jibia
Sakataren ƙaramar hukumar, an dakatar da shi ne a lokacin da Majalisar zartaswa ta ƙaramar hukumar ta yi wani zama a ranar Alhamis 13 ga watan Yuni 2024.
Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa ɗauke da sa hannun Abdulsalam Iro, shugaban majalisar zartarwar ta ƙaramar hukumar tare da rabawa Manema Labarai.
Katsina Post ta samu cewa, an dakatar da sakataren tare da sanya hannun ‘yan majalisar zartarwar a ƙaramar hukumar ta Jibia dake jihar Katsina.
Bayan doguwar tattaunawa da ta yi, majalisar ta yanke hukuncin tuhumar sakataren ƙaramar hukumar da zama sakataren na tsawon makonni biyu wanda hakan zai baiwa ‘yanmajalisar damar binciken wasu ayyuka guda 3, da suka haɗa da;
Tuhumar sa a kan yadda ya rarraba kayan Abinci na gwamnatin tarayya ga al'ummar yankin, sai kuma yadda yake wakiltar shugaban ƙaramar hukumar akan batutuwa da dama, da kuma yadda yake gudanar da ayyukan da ƙaramar hukumar ta ba shi.