An Kawo Sabon Shugaban Hukumar Gidajen Gyaran Hali A Katsina

Katsina Ta Yi Sabon Shugaban Hukumar Gidajen Gyaran Hali

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

Ahmad A. Usman

An Kawo Sabon Shugaban Hukumar Gidajen Gyaran Hali A Katsina

Ahmed Abdu Usman ya za ma sabon shugaban hukumar gidajen gyaran hali a Katsina, inda ya karɓi takardar a hedikwatar su da ke jihar Katsina.

Katsina Post ta samu cewa, an miƙawa tsohon shugaban hukumar Muhammad A. Haruna, mai barin gado takardar canja shi a jihar tunda farko.

Jami'in Hulda da Jama'a na Rundunar jihar Katsina, ASC Najib Idris Kunduru, shi ne ya bayyana haka ga Manema Labarai.

Da yake jawabin bankwana, CC MA Haruna ya yabawa ma’aikatan hukumar bi sa goyon baya da haɗin kai da suka ba shi a tsawon lokacin da ya ya yi a rundunar, Ya kuma buƙace su da su ba wanda ya gaje da haɗin kai fiye da yadda suka ba shi a jihar.

Da yake jawabi ga jami'an, sabon shugaban ya yi alƙawarin ƙarfafa nasarorin da magajin sa ya samu, tare da neman haɗin kai da goyon bayan ɗaukacin ma’aikatan, wajen ganin ya aiwatar da aikin da ya dace a faɗin jihar Katsina.