APC Ki Fara Tattara Kayanki Tun Kafin Zaɓen 2027- Inji Sabon Shugaban Jam'iyyar PDP A Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Monday, 02 Sep, 2024
APC Ki Fara Tattara Kayanki Tun Kafin Zaɓen 2027- Inji Sabon Shugaban Jam'iyyar PDP A Katsina
A cikin jawabin sabon shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina, Hon. Nura Amadi Kurfi, ya ce jam'iyyar APC ta gaggauta tattara kayanki tun kafin zaɓen 2027 a kowacce mataki.
An zaɓi matashin ɗan siyasa, kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kurfi, Nura Amadi-Kurfi, wanda ya zama sabon shugaban jam’iyyar PDP a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar, a hedikwatar jam’iyyar da ke kan hanyar Katsina zuwa Kano.
Shugaban kwamitin da uwar jam’iyyar PDP ta turo daga Abuja domin gudanar da zaɓen, Ilu Bello ne ya bayyana haka, bayan kammala jefa ƙuri’u da wakilan jam’iyyar da suka fito daga lungu da saƙon jihar Katsina.
Da ya ke jawabi, sabon shugaban Jam’iyyar, Nura Amadi-Kurfi, wanda ɗa ne ga fitaccen ɗan siyasar nan, Amadi Kurfi, ya sha alwashin kawar da jam’iyyar APC da ke mulkin jihar Katsina, domin fitar da al’umma halin yunwa da rashin tsaro da kuma talauci da al’ummar ke fama da su.
Ya ce, sun kafa ɗan-ba na yin aiki tuƙuru domin korar APC daga mulki, idan ma ba su shirya ba, su sani domin shi ya yi ɗamara.
Ya ƙara da cewa, duk da ƙalubalen da jam’iyyar PDP ke ciki a jihar Katsina, zai yi bakin ƙoƙari sa don ganin sun leƙa gida-gida da zimmar haɗa kan masu kishi da kyakkyawar niyya, sun dawo cikin ta, domin tafiya tare da kuma dawo da martabar jam’iyyar PDP a jihar.
A cewar sa, PDP a jihar Katsina ba baƙuwar jam’iyya ba ce, har shugaban ƙasa sun yi daga jihar Katsina, idan akai duba da irin shugabancin Malam Umaru Musa Yar'adua.
Ya cigaba da cewa a ƙarƙashin jagorancin da Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke da yake yi, shi ne ya sa jam’iyyar PDP ta dawo hannun jama’a a karon farko, wanda abin a yaba ne. Don haka ya zama wajibi su haɗa kai don ganin sun amshe mulkin jihar Katsina daga hannun APC.
Tunda farko, ya miƙa godiya ta musamman ga jagoran PDP na jihar Katsina, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke da kuma wakilai da suka fito daga mazaɓu 361 waɗanda suka jefa masu ƙuri’a da sauran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP na jihar Katsina da kuma wakilan Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, reshen jihar Katsina wadda ta sanya idanunta kan yadda zaɓen ya gudana.