'Yansandan Katsina sun yi ma 'Yanbindiga taron dangi a Kankara

Jami'an tsaro sun ɗakile wani hari da 'Yanbidaga suke shirin yi a ƙanƙara

Police

'Yansandan Katsina sun yi ma 'Yanbindiga taron dangi a Kankara

Rundunar 'Yasandan jihar Katsina haɗin guiwa da jami'an KCWC da 'Yanbanga, sun daƙile wani hari da 'Yanbindiga suka kai a yankin ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

A lokacin da rundunar hedikwatar ‘yansandan yankin Kankara ta samu labarin wasu 'Yanbindiga, suna shirin shiga ƙauyen Gidan Dan-Ali ɗauke da muggan makamai, da jin labarin haka nan da nan Baturen Dansanda CSP Iliyasu Ibrahim, ya yi gaggawar tara tawagar da suka hada da jami’an 'Yansanda, jami'an KSCWC, da 'Yanbanga zuwa wurin a ranar Talata 16 ga watan Yuli, 2024 domin daƙile harin.

Lokacin da haɗakar jami'an tsaron suka bi sahun maharan zuwa ƙauyen Bulunkuza da ke unguwar Tudun Wada a yankin ƙaramar hukumar, hakan ya tilastawa 'Yanta'addar tsorata da kuma yin watsi na yunkurin kai harin taaddancin.

Katsina Post ta samu cewa, jami'an sun samu nasara ga 'yanbindigar, tare da halaka wani da ake zargin ɗanfashi da makami ne. Haka kuma sun ƙwato Bindiga ƙirar AK47 a lokacin gumurzun.

Idan ma su bibiyar rahotanni ba su manta ba, ƙaramar hukumar Kankara tana cikin jerin ƙananan hukumomin da suke fama da Iftila'in matsalar tsaro a jihar Katsina, wanda a wani lokaci yake yin ƙamari wani lokaci kuma a samu sauƙi lokaci-lokaci.


Comment As:

Comment (0)