'Yansanda sun kai samame a maboyar 'yanbindiga, sun kubutar da mutum 30 a Katsina

Rundunar 'yansandan Katsina ta ceto mutane da yawa a wajen 'Yanbindiga

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

Police

'Yansanda sun kai samame a maboyar 'yanbindiga, sun kubutar da mutum 30 a Katsina

Jami'an tsaro a Katsina sun kai wani samame a maɓoyar 'yanbindiga a wani yanki a jihar.

A wani ɗauki-ba-daɗi da rundunar ‘yansandan jihar Katsina ta kai a ranar 21 ga watan Agusta, 2024, inda suka kai farmaki maɓoyar ‘yan bindiga da ke tsakanin ƙananan hukumomin Dutsinma da Safana, inda suka ceto wasu mutane 7 da aka yi garkuwa da su.

Sun kai samamen a wasu ƙauyuka biyu a ƙaramar hukumar Dutsinma a ranar 17 ga watan Agusta, 2024. tare da ƙwato Bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya.

Rundunar ta yi nasara ne ta haɗin guiwar tawagar ‘yansanda da ke hedikwatar ‘yansandan Dutsinma da ‘yanbanga ƙarƙashin jagorancin DPO, CSP Bello Abdullahi Gusau.

Katsina Post ta samu cewa, rundunar sun yi nasarar kuɓutar da su ba tare da sun samu rauni ba, inda aka garzaya da su Asibiti mafi kusa domin kula da lafiyarsu. Haka kuma an samu nasarar ƙwato Bindiga ƙirar AK47 guda ɗaya a yayin da ake gudanar da aikin.

Hakazalika, daga cikin nasarar da rundunar ta ƙara samu, inda ta samu kiran gaggawa a hedikwatar ‘yansanda ta Jibia cewa ‘yanbindiga ɗauke da muggan makamai suna harbe-harbe a kauyukan Jibia, Maje, Nasarawa, da kuma Lankwasau a lokaci-lokaci a ƙaramar hukumar.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, da samun rahoton DPO Jibia ya haɗa tawagar jami’an tsaro tare da kai ɗaukin gaggawa suka yi wa ‘yanbindigar kwanton ɓauna.

Tawagar ta yi nasarar daƙile dukkan hare-haren uku tare da ceto mutane Uku da aka yi garkuwa da su. Sai dai an garzaya da waɗanda harin ya rutsa da su Asibiti domin kula da lafiyarsu saboda sun samu ƙananan raunuka sakamakon harin.

A cewar mai magana da yawun rundunar, bugu da ƙari, a ranar 20 ga watan Agusta, 2024, sun samu a hedikwatar Malumfashi, inda wasu ‘yanbindiga ɗauke da muggan makamai suka kai hari ƙauyen Yaba, ƙaramar hukumar Malumfashi, suka yi garkuwa da mutane ashirin 20 tare da yin garkuwa da su da Shanu 5.

Ya jaddada cewa, da samun rahoton, ba tare da bata lokaci ba DPO Malumfashi ya shirya tawagar jami’an ‘yansanda inda suka kai ɗauki tare da gumurzun wuta da ‘yanbindigar a wajen kauyen yayin da suke ƙoƙarin tserewa tare da waɗanda abin ya shafa.

Rundunar ta yi babbar nasara ga ‘yanbindigar inda suka daƙile harin, tare da kuɓutar da duk waɗanda aka yi garkuwa da su tare da ƙwato dabbobin da aka yi garkuwa da su yayin da ‘yanbindigar suka tsere da raunukan harsasai daban-daban a jikin su.