'Yansanda Sun Kuɓutar Da Yaron Da Akai Garkuwa Da Shi A Katsina
Jami'an tsaro sun kuɓutar da yaro ɗan shekara Shida da akai garkuwa da shi a Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Thursday, 22 Aug, 2024
'Yansanda Sun Kuɓutar Da Yaron Da Akai Garkuwa Da Shi A Katsina
Rundunar 'Yansandan jihar Katsina ta yi nasarar cafke wani Matashi da ake zargin ya yi garkuwa da wani Yaro mai shekaru 6 a jihar Katsina.
Tun da farko, a ranar 17 ga watan Agusta, 2024, rundunar ta samu wani bayanan sirri, inda rundunar ta samu nasarar cafke matashin mai suna Halilu Yusuf, mai shekaru 21 da take zargi da aikata laifin.
Katsina Post ta samu cewa, matashin ɗan asalin garin Gesawa ta ƙauyen Shinkafi ta jihar Katsina, wanda ake zargin sa da laifin sace wani yaro ɗan shekara Shida a Duniya.
Wanda ake zargin ya yi garkuwa da yaron ne a unguwar Kofar Sauri inda ya buƙaci mahaifin yaron da ya biya kuɗin fansa kimanin Naira Miliyan 2,000,000.00 domin a sako shi, kamar yadda aka kiran waya da ba a san sunanan ko waye ba.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce, samun rahoton haka ke da wuya, cikin gaggawa DPO GRA Katsina ya tattara jami’an tsaro tare da yunƙurin kuɓutar da wanda aka sace.
A cewar sa, an yi nasarar zaƙulo wanda ake zargin tare da kama shi, kuma an kuɓutar da wanda aka sace lafiya Lau ba tare da ƙwarzane ba, ya ce a yayin gudanar da bincike, waɗanda ake zargin sun amsa laifin aikata laifin kuma rundunar na ci gaba da gudanar da bincike.