'Yansanda Sun Kama Matashin Da Ya Sare Hannun Mahaifinsa A Katsina
An kama matashin da ya sare ma ƙanen mahaifinsa hannu a Katsina
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Friday, 23 Aug, 2024
'Yansanda Sun Kama Matashin Da Ya Sare Hannun Mahaifinsa A Katsina
Matashin da ya zabtare hannun ƙanen mahiafinsa a jihar Katsina ya shiga hannu 'Yansanda.
Wani matashi da ya sare ƙanen mahaifinsa da Adda a hannu bisa zargin Maita ya shiga hannun ’yansanda a garin Jangefe da ke ƙaramar Hukumar Batagarawa a jihar Katsina.
Kakakin rundunar ’yansanda ta jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, shi ne ya shaida ma Manema Labarai haka a yayin gabatar da matashin lokacin gabatar da masu manyan laifuka a jihar.
ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce bayan samun labarin abin da ya faru suka yi nasara kama wanda ake zargi da saran kanen mahaifin nasa, kuma bayan sun gama bincike za su tura shi zuwa kotu domin yanke mishi hukunci.
Kamar yadda ya fada da bakinsa, matashin ya ce yana zargin ƙanen mahaifin na sa da maita, inda yake kama ’yan gidansu, ciki har da mahaifiyar matashin.
Kamar yadda Katsina Post ta samu daga Aminiya, matashin ya ce mahaifiyarsa ta kamu da rashin lafiya bayan shigowar ƙanen mahaifin nasa gidan ya fita, kuma ta riƙa ambaton sunan ƙanen mahaifin na sa.
Ya ƙara da cewa, da ma duk wani ɗan gidansu da ya kamu da rashin lafiya sai ya riƙa ambaton sunansa. Wannan ne ya sa yake zargin sa da yin maita.
A cewarsa, ya je gidan ƙanan mahaifin nasa ne inda bayan ya yi mashi sallama ya fito ya nemi su keɓe domin yana son magana da shi, amma sai ya ƙi yarda ya bi shi inda ya so su je.
Nan take ya bayyana mishi zargin da yake masa, sannan ya kai mishi sara da addar dake hannunsa, kuma ya same shi a hannu.