'Yanbindiga Sun Kashe Jami'an KSCWC A Jihar Katsina
'Yanbindiga sun kashe jami'an KSCWC a jihar Katsina An kashe jami'an sa kai na Community Watch Corp
- Posted By: Zaharaddeen Gandu --
- Monday, 12 Feb, 2024
- Reporter : zaharaddeen Gandu
'Yanbindiga sun kashe jami'an KSCWC a jihar Katsina
An kashe jami'an sa kai na Community Watch Corps da ke aikin tsaron al'umma da taimakawa gameda samar da tsaro a jihar Katsina su biyu a garin Maidabino dake a yankin ƙaramar hukumar Danmusa.
Majiyar mai tushe ta ce 'yan ta'adda sun yi wani samame da sanyin safiyar ranar Juma'ar 09 ga watan Fabrairu 2024 a garin Maidabino, inda aka tabka gumurzu tsakanin jami'an da 'yanbindigar har jami'an 2 suka rasa ransu.
Bayan mutuwar jami'an an gudanar da jana'izarsu, inda ɗayan mamacin aka gudanar da jana'izar sa tun ƙarfe 7 na safe, a yayin da shi ma gudan aka gudanar da jana'izar sa bayan sun harbeshi da misalin karfe 11 na safiyar juma'a.
Kamar yadda Katsina Post ta samu daga DCL Hausa, ya zuwa lokacin haɗa rahoton babu cikakken daga wajen 'yan sa kan gameda nasarar hallaka wasu daga cikin 'yan ta'addar da suka kai musu hari.
Saide, mai Magana da yawun rundunar 'yansandan jihar Katsina ASP Sadiq Abubakar Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya ce ɗanbanga ɗaya ne aka kashe, sai aka raunata ɗan sa kai na Community Watch Corps guda ɗaya.