Ƴan Bindiga Sun Tarwatsa Masallata Ana Hudubar Jumma’a a A Katsina

×

Get latest updates Sign up to our newsletter

Name   *
Email   *
Phone   *
Category   *
Frequency   *

undefined

Wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki ana tsaka da sallar jummua a garin Dan-Ali da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina, inda suka tarwatsa masallata.

Kamar yanda Katsina Post ta samu, maharan dauke da makamai sun kutsa kai cikin garin, inda suka rika harbe-harbe, lamarin da ya haifar da firgici tare da tilasta wa masu ibadar gudu.

Wani mazaunin garin ya tabbatar da afkuwar faruwar lamarin inda yace “Muna cikin Sallar Juma’a ne muka ji harbin, sai kowa ya ruga da gudu. Ba kammala sallar ba. Godiya ga jami’an tsaro da ke yankin da suka fatattake su”

Majiyar, wacce ta bukaci a sakaya sunanta, ta kara da cewa, "Muna bukatar karin jami’an tsaro a garin saboda 'yan bindigar sun addabbi yankin namu”

A cewarsa, sama da mako guda ‘yan bindiga ke hana manoma shiga gonakinsu a yankin Dan-Ali da kewaye, ciki har da Gwarjo, da kasuwar, da Tudun, da Tasha Kadanya, da Tasha Biri.

Majiyar ta kara da cewa "An yi garkuwa da manoma da yawa, kuma dukkanmu muna tsoron shiga gonakinmu."

Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Sadiq, ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoto.