‘Yan sanda sun kama mutum 22 kan zargin sata a Katsina
‘Yan sanda sun kama mutum 22 kan zargin sata a Katsina
- Posted By: Mustapha Saddiq --
- Saturday, 07 Sep, 2024
Rundunar ƴan sanda a Katsina sun kama mutane guda 22 da ake zargi da aikata sace-sace da lalata kayan gwamnati.
Acikin mutanen har da mace yar shekara 40 da ake zargi da sayen kayan satar.
Jami’in yaɗa labarai na hukumar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana haka bayan ya baje masu laifukan a gaban manema labarai a shelkwatan ƴan sanda na Katsina.
Ya faɗi sunan Hamza Lawal da ake kira Honorabul da ke zaune a titin kwaɗo da Safiyanu sun shiga wani gida a Modoji quarters tare da taimakon Ahmed Muhammad suka kwashe kayan gidan gaba ɗaya.
Kayan da suka sace a gidan zasu kai kuɗi Naira miliyan 10 waɗanda suka haɗa da manyan talabijin na bango guda uku da na’urar sanyaya ruwa (freezer) da kujeru na alfarma da sauran su.
ASP Sadiq ya cigaba da cewa, binciken da suka yi sun gano cewa wani matashi Aminu Musa tuni ya ranta a na kare tare da Mariya da ke zaune a Katsina da Batagarawa waɗanda su ke taimakawa ɓarayin .
Tuni dai kamar yadda jami’in yaɗa labarai na ƴan sandan ya tabbatar da samun nasarar kama masu aikata laifin, kuma sun tabbatar da cewa su suka shiga wannan gida suka aikata satar.
Haka kuma, ya ce mutum 12 cikin waɗanda aka kama an same su ne da sace wayoyin rodi na wutan lantarki masu amfani da hasken rana.
Ya ce, wani matashin ne yayi wa ƴan sanda kwarmatan ɓarayin inda nan take suka kai sane a Sha’iskawa Quarters inda nan suka kama ɓarayin da suka samu da wayoyin wutan lantarki da rodi tare da sauran muggan makamai.
Kazalika, mutane 7 daga cikin ɓarayin sun gudu inji ASP Sadiq, amma ƴan sanda na ƙoƙarin gano su domin su fuskanci Shari’a.
Da zarar ƴan sanda sun gama bincike za a gurfanar da masu laifin a kotu.